14 Maris 2020 - 05:56
​Jagora Ya Bada Umurni Na Musamman Dangane Da Yaki Da Cutar Corona Virus

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyeed Aliyul Khamina’e ya umurci babban hafsan hafsoshin sojojin Iran da ya kafa sansani na musamman don gabatar da ayyukan kiwon lafiya ga mutanen kasar don yaki da cutar...

(ABNA24.com) Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyeed Aliyul Khamina’e ya umurci babban hafsan hafsoshin sojojin Iran da ya kafa sansani na musamman don gabatar da ayyukan kiwon lafiya ga mutanen kasar don yaki da cutar Corona Virus ta watsu a ko ina a cikin kasar. Musaman ganin cewa akwai shaidu da suke nuna cewa cutar ta Corona hari ne da kyayoyin halitta.

Jagoran ya bukaci Janar Baqiri ya tabbatar da cewa dukkan ayyukan kiwon lafiyan da sojojin kasar suke bayarwa ya kasance daga cibiya guda da kuma shugabanci guda daya.

Jagoran ya kara da cewa akwai bukatar a tsara ayyukan yaki da kuma hana karin yaduwar wannan cutar ta yadda zai zama wata makaranta ce ta karfafa sojojin kasar a korewar yaki da makamai na kwayoyin cuta.



/129